Zanen Ra'ayi, fitowar rana
Zanen Ra'ayi, fitowar rana | ||||
---|---|---|---|---|
painting (en) | ||||
Bayanai | ||||
Farawa | 1872 | |||
Suna a harshen gida | Impression, soleil levant | |||
Laƙabi | Impression, soleil levant da Impression, Sunrise | |||
Motsi | Zanen Ra'ayi | |||
Mamallaki | Musée Marmottan Monet (en) , Ernest Hoschedé (en) da Georges de Bellio (en) | |||
Nau'in | marine art (en) | |||
Maƙirƙiri | Claude Monet | |||
Gagarumin taron | sales (en) da art theft (en) | |||
Catalog code (en) | 63, 263 da 98 | |||
Kayan haɗi | oil paint (en) da canvas (en) | |||
Collection (en) | Musée Marmottan Monet (en) | |||
Inventory number (en) | 4014 | |||
Exhibition history (en) | 1st impressionist exhibition (en) | |||
Location of creation (en) | Le Havre | |||
Copyright status (en) | public domain (en) | |||
Inscription (en) | Claude Monet.72 | |||
Wuri | ||||
|
Zanen Ra'ayi, fitowar rana wato Impression, Sunrise ( Faransanci : Impression, soleil levant ) wani zane ne na shekarar 1872 wanda Claude Monet ya fara nunawa wanda daga baya ya zamo sananne da "Baje kolin Zanukan Ra'ayi" a Paris a cikin watan Afrilun,shekara ta 1874. An kuma ba da kyautar zanen tare da ƙarfafa sunan Kungiyar masu Zanen Ra'ayi.
Zanen Impression, Sunrise yana nuna tashar jirgin ruwa na Le Havre, garinsu Monet. Yanzu ana nuna su a Musée Marmottan Monet a Paris. [1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Monet ya ziyarci garinsu wato Le Havre a arewa maso yammacin Faransa a cikin shekarar 1872 kuma ya ci gaba da ƙirƙirar jerin ayyuka da ke nuna tashar jirgin ruwa na Le Havre. Littattafan zanukan guda shida suna nuna tashar jirgin ruwa ne a lokaci daban daban "da asubahi, da rana, da maraice, da dare kuma daga ra'ayoyi daban-daban, wasu daga ruwan da kansa wasu kuma daga ɗakin otal suna kallon tashar jirgin ruwan".[2]
Zanen Impression, na Fitowar Rana ya zama mafi shahara a cikin jerin zanukansa bayan da aka fara gabatar dashi acikin watan Afrilun 1874 a Parisa a wani nuni da kungiyar "Masu Zane, Masu Sassaka, da dai sauransu. Inc." Daga cikin mahalarta talatin, Monet, Edgar Degas, Camille Pissarro, Pierre-Auguste Renoir, da Alfred Sisley ne suka jagoranci baje kolin, kuma sun nuna ayyuka sama da ɗari biyu waɗanda kusan mutane 4,000 suka gani, ciki har da wasu masu sukar rashin amincewa da salon.[3]
A cikin shekarar 1985 Philippe Jamin da Youssef Khimun ne suka sace zanen daga Musée Marmottan Monet . An dawo da shi kuma ya koma gidan kayan tarihi a shekarar 1990,[4] kuma an sake nuna shi a cikin shekara ta 1991.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Impression, Sunrise, Musée Marmottan Monet
- ↑ Brettell, Richard R. (2000). Impression : painting quickly in France 1860-1890. New Haven [u.a.]: Yale Univ. Press [u.a.] p. 126. ISBN 0300084463.
- ↑ Tomlinson, Janis, ed. (1995). Readings in nineteenth-century art. Upper Saddle River, N.J.: Prentice Hall. ISBN 0-13-104142-8.
- ↑ "The World's Greatest Art Heists". Forbes. 12 February 2008. Retrieved 16 November 2010.
- ↑ "Travel Advisory - Stolen Paintings Back in Paris Heists". The New York Times. 28 April 1991. Retrieved 16 November 2010.