(Translated by https://www.hiragana.jp/)
Sudan na cikin barazanar yunwa mafi muni cikin shekaru 40 - Amurka
Isa ga babban shafi

Sudan na cikin barazanar yunwa mafi muni cikin shekaru 40 - Amurka

Mahukuntan Amurka sun yi gargaɗin cewa matsalar yunwa da ƙasar Sudan ke fuskanta ka iya yin muni fiye da wadda aka taɓa gani kasar Habasha, shekaru 40 da suka gabata.

Yaƙi ya ki ci ya ki cinyewa a Sudan
Yaƙi ya ki ci ya ki cinyewa a Sudan Reuters/Margaret Aguirre/International Medical Corps/Handout
Talla

Gargaɗin na zuwa ne, yayin da ɓangarorin da ke yiwa juna kallon hadarin kaji a ƙasar ke ci gaba da ƙazamin rikicin da suka kwashe tsawon lokaci suna fafatawa.

A cewar Jami’an na Amurka, bangarorin biyu, na daƙile yunƙurin shigar da kayayyakin agaji zuwa cikin ƙasar, duk da irin ƙoƙari da ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasa da ƙasa ke yi na ganin sun shigar da kayayyaki ga sassan ƙasar.

A halin yanzu dai, hankalin ƙasashen duniya ya koma kan Gaza, da ake fuskantar matsananciyar yunwa.

Sai dai mahukuntan Amurkan na gargaɗin cewa, matuƙar hankalin mai yanka kaba bai koma ga rina ba game da halin da Sudan ɗin ke ciki, wadda ta shafe tsawon lokaci a jerin ƙasashen da suka fi fuskantar matsalolin jin kai a duniya, nan da ƙanƙanin lokaci zata iya kawo ƙarshen tarihin matsananciyar yunwa da aka taɓa fuskanta a Habasha shekaru 40 da suka gabata.

Tuni dai yaƙin basasar na Sudan ya kashe mutane aƙalla dubu 14, tare da tilastawa wasu miliyan 10 barin barin muhallansu.

A makon da ya gabata ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci da a kawo ƙarshen mamayar da dakarun RSF suka yi wa El Fasher, kusan watanni 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.