(Translated by https://www.hiragana.jp/)
Tarihin J.D Vance da Trump ya zaɓa a matsayin mataimakinsa
Isa ga babban shafi

Tarihin J.D Vance da Trump ya zaɓa a matsayin mataimakinsa

A jiya Litinin ne Donald Trump ya bayyana Sanata J. D Vance mai tsattsaurar ra’ayi daga jihar Ohio a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugabancin ƙasar da ke tafe cikin watan nuwamba mai zuwa.

J.D. Vance
J.D. Vance REUTERS - Gaelen Morse
Talla

An haifi James David Vance, a ranar 2 ga watan Agustan 1984, a birnin Ohio da ke Amurka.

Ya yi karatunsa na firamare da Sakandire a Ohio, inda ya kammala a shekarar 2003, daga bisani ya shiga Jmai’ar Jihar Ohio, inda ya yi karatun digirinsa na a ɓangaren kimiyyar siyasa da kuma Falsafa ya kuma kammala a shekarar 2009.

Idan muka koma baya kaɗan bayan kammala Sakandire a shekarar 2003, ya samu horon zama sojan Amurka na musamman.

Trump da Vance
Trump da Vance © Charles Rex Arbogast / АР

Kasancewar J.D marubuci ya rubuta litattafai da dama, a watan Yulin shekarar 2021 ne ya fara yaƙin neman zaɓen zaman ɗan takarar sanata a Jam’iyyar Republican, inda ya lashe zaɓen fidda gwanin jam’iyyar da aka yi na ranar 3 ga watan Mayun 2022, wanda hakan ya ba shi damar samun nasara a babban zaɓen.

A ranar 3 ga watan Janairun 2023 ne aka rantsar da a matsayin ɗan majalisar Dattawan Amurka mai wakiltar Jihar Ohio.

James David Vance, dai ya shafe tsawon lokaci yana caccakar manufofin tsohon shugaban Amurkan Donald Trump, wanda a jiya ya bayyana sunan sa a matsayin abokin takararsa, a zaɓen  da ke tafe na watan Nuwamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.