(Translated by https://www.hiragana.jp/)
Anas bn Malik - Wikipedia Jump to content

Anas bn Malik

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anas bn Malik
Rayuwa
Haihuwa Madinah, 611
ƙasa Khulafa'hur-Rashidun
Khalifancin Umayyawa
Mutuwa Basra, 713
Ƴan uwa
Mahaifiya Umm Sulaym bint Milhan
Abokiyar zama Q12214930 Fassara
Yara
Ahali Al-Bara' ibn Malik (en) Fassara, Q106814584 Fassara da Q89384455 Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Harsuna Larabci
Malamai Muhammad
Abu Hurairah
Muadh ibn Jabal
Abu Dhar al-Ghifari
Salman al-Farsi
Abdullahi dan Abbas
Abu Musa al-Ashari
Abdullah dan Masud
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a Islamic jurist (en) Fassara, muhaddith (en) Fassara da rawi (en) Fassara
Aikin soja
Ya faɗaci Yaƙin Khaybar
yaƙin Hunayn
Nasarar Makka
Siege of Ta'if (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Mabiya Sunnah

Anas bn Malik bn Naḍr al-Khazrajī al-Ansārī ( Larabci: أنس بن مالك الخزرجي الأنصاري‎ (c.612 – c.712 [1] ) sanannen sahabi ne na Annabi Muhammad (S.A.W.)

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Anas bn Malik dan kabilar Najjar ne, kabilar Khazraj daga Yathrib. An haife shi shekaru goma kafin hijira Annabi Muhammad (S.A.W.). Bayan mahaifinsa, Malik bn Nadr, ya rasu ba musulmi ba, mahaifiyarsa, Umm Sulaim, ta sake yin aure zuwa wani sabon tuba, Abu Talha ibn Thabit. Kanin Anas daga wannan auren shine Abdullahi bn Abi Talha.

A Lokacin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya isa Madina a shekarar 622, mahaifiyar Anas ta gabatar da shi ga Annabi Muhammad (S.A.W) a matsayin bawa a gare shi. [1]

Bayan wafatin Annabi Muhammad a shekara ta 632, Anas ya shiga yakin mamaya. [1] Shi ne na karshe daga cikin fitattun Sahabban Manzon Allah ( SAW) da ya rasu, bayan shakaru 80 da rasuwar Annabi Muhammadu (SAW). Anas ya rasu a shekara ta 93 bayan hijira (712 miladiyya) a garin Basra [2] yana da shekara 103 (watau). [2]

  1. 1.0 1.1 1.2 Finding the Truth in Judging the Companions, 1. 84-5; EI2, 1. 482 A. J. Wensinck J. Robson
  2. 2.0 2.1 T. P. Hughes, 1885/1999, Dictionary of Islam, New Delhi: Rupa & Co.