Wole Soyinka
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Akinwande Oluwole Babatunde Soyinka(Yarbanci: Akínwándé Olúwo̩lé Babátúndé S̩óyíinká; an haife shi ne a ranan 13 ga watan Yulin shekara ta 1934), wanda aka sani da Wole Soyinka (lafazin [wɔlé ʃójĩnká]), ɗan wasan kwaikwayo ne na Nijeriya, mawaƙi kuma marubuci. An ba shi lambar yabo ta Nobel ta adabi a shekara ta 1986, mutum na farko a sub-saharan Africa da aka girmama a wannan rukunin. An haifi Soyinka a cikin dangin Yarbawa a Abeokuta. A 1954, ya halarci Kwalejin Gwamnati a Ibadan, sannan ya halarci Kwalejin Jami'ar Ibadan da Jami'ar Leeds a Ingila. Bayan ya yi karatu a Najeriya da Ingila, ya yi aiki tare da gidan wasan kwaikwayo na Royal Court da ke Landan. Ya ci gaba da rubuta wasannin kwaikwayo waɗanda aka samar a ƙasashen biyu, a gidajen kallo da rediyo. Ya taka rawar gani a tarihin siyasar Najeriya da gwagwarmayar neman 'yanci daga Burtaniya. A shekarar 1965, ya kwace gidan watsa labarai na Yammacin Najeriya ya watsa shirye-shiryen neman a soke zaben yankin Yammacin Najeriya. A shekara ta 1967, a lokacin yaƙin basasar Najeriya, gwamnatin tarayya ta Janar Yakubu Gowon ta tsare shi tare da sanya shi a kurkuku na tsawon shekaru biyu.