(Translated by https://www.hiragana.jp/)
Ilimi - Wikipedia Jump to content

Ilimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
sani
philosophical concept (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na ma'ajiya
Has cause (en) Fassara koyo, qualia (en) Fassara da Wahayi
Karatun ta Epistemology, theory of knowledge (en) Fassara, sociology of knowledge (en) Fassara da falsafa
Contributing factor of (en) Fassara understanding (en) Fassara da competence (en) Fassara
Has characteristic (en) Fassara knowledge environment (en) Fassara, limits of knowledge (en) Fassara da knowledge type (en) Fassara
Tarihin maudu'i history of knowledge (en) Fassara
Amfani wajen knowledge management (en) Fassara
Hannun riga da ignorance (en) Fassara
Dalibai masu koyan ilimi
Dalibai

Ilimi na nufin sani akan wani abu ko kuma kwarewa a wani abu, ko aikace, ko, kuma yana iya zama sanin wani abu ko wani yanayi.

manhajar Koyar da yara

Akan yi wa ilimi kirari da cewa:

  • "Ilimi garkuwar Dan Adam."
  • "Ilimi Hasken rayuwa."
  • "Ilimi kogi ne"
  • "Aikin mai ilimi yai daba dana  jahili
  • Ilimi kesa aci riban duniya da lahira
    "Rayuwa mai kyau baiyuwuwa idan ba ilimi

Ma'anar Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Ma'anar ilimi a sauƙaƙaƙƙen harshe shine "sani" wato sanin abubuwan da suke gaskiya, saɓanin ra'ayi. Bayanin da yake dai-dai shi ne ilimi. Ilmi ko yaushe ana iya goyan bayansa da shaida. Idan kuma ba a tabbatar da magana da hujja ba, to ba ilimi ba ce.

Ilmi na iya komawa ga fahimtar ka'ida ko kuma fahimtar aikata wani batu. Wannan shi ne batun bambancin Ra ayi tsakanin "sanin haka" da "sanin yadda" Yana iya zama a fakaice (kamar yadda yake da fasaha mai amfani ko ƙwarewa) ko a bayyane (kamar yadda tare da fahimtar ka'idar batun); yana iya zama fiye ko kasa da na yau da kullun ko na tsari. A cikin falsafa, ana kiran binciken ilimi epistemology. Masanin falsafar Plato ya bayyana ilimi a matsayin “ gaskatawar gaskiya”. Wannan ma'anar ita ce batun matsalolin Getier.

Hanyoyin Samun Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Bincike.

Bincike hanya ce ta samu ilimi a wannan zamani da ba kamarta.

  • IYAYE

Hanya ta farko: Iyaye; Ana fara samun ilimin farko ne daga iyaye, musamman Mahaifiya. Daga gareta ne mutum yake fara koyar abubuwa iri-iri. Kamar su cin abinci, sanya tufafi, tarbiyyar rayuwa, tsafta da dai sauransu. Da taimakon mahaifi kuma yaro ya ke samun Juriya, Dogaro da Kai, Nagarta da kuma tabbatuwa a kan turba ta gari.Sannan ne yasa masu iya dance sukace mahaifiyya itace malamar farko ta kowa ne mutum.

  • DANDALI.

Hanya ta biyu: Ita ce Dandali ko kuma mu ce rariya ko kan layi. Anan ne yaro yake koyon gane wadansu mutane daban da na gidan su. Kuma a nan ne yaro yake koyon wasanni da koyon zama da jama'a daban.

  • MAKARANTA.

Hanya ta uku: Makaranta; Daga hannun Iyaye kuma, sai makaranta. Anan mutum ya ke koyon ilimin Addini dana Boko. A Makarantar ne za a koyawa mutum ilimi daban-daban, tun daga Firamare zuwa Sakandire, har zuwa Jami'ah. A nan a ke samun shaidar karatu babba da karama don aiki a manya ko kananan ma'aikatu.

Nau'o'in Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Nau'o'in ilimi ya kasu ne zuwa gida uku kamar yarda masana suka tsara su.

  • ILIMIN ZAMANI (boko).
  • ILIMIN ADDINI.
  • ILIMIN GARGAJIYA.

Yanzu zamu dauko su daya bayan daya mudan tattauna akan su, amma a takaice.

Iimin Zamani (boko)

[gyara sashe | gyara masomin]

Shi ilimin zamani ko kuma muce boko kamar yarda akasarin hausawa muke kiran shi. Ya samo asaline daga Turawa wadanda suka yi mulkin mallaka a kasar mu Najeriya.

Turawan kasar Ingila su ne suka kawo mana ilimin boko a kasarmu ta Najeriya. Sun fara kaddamar da tsarin ilimin boko ne a sashen kudancin Najeriya kafin su gabatar da shi a yankin Arewacin Najeriya. Duk da dai lokacin turawa sun sha wahala harma da yake-yake kafin samun nasarar kaddamar da ilimin zamani a yankin Arewacin Najeriya amma kuma yanzu jama'ar yankin sun karbeshi hannu bibbiyu.

  • tsarin ilimin boko

Ilimin boko ilimine wanda yake da tsare tsare kafin, bayan da kuma lokacin da ake koyar da shi. Akwai tsare-tsare kafin a koyar da ilimin boko, kamar hukumomi daban-daban na ilimi su tsara abin da za'a koyar a shekara-shekara, zangunan karatu da kuma sati-sati, wanda ake kira da (SYLLABUS) a harshen Turanci. Sannan malami yana da tsare-tsaren da zai yi kafin shigar shi cikin aji wanda ake kira [LESSON PLAN] da kuma [LESSON NOTE] a turance.

Ilimin Addini

[gyara sashe | gyara masomin]

Ilimin addini, ilimine da ya samo asali bayan zuwan addinin Musulunci a Kasar Hausa .

  • tsarin Ilimin Addini.

Hanyar da ake bi wajen koyar da ilimin addini a gargajiya shine, idan yaro ya kai kamar shekara bakwai da haihuwa. Ana kaishi makarantar Alkur'ani wadda akafi sani da makarantar allo . Bayan yaro yayi saukar Kur'ani kuma, sai ya tafi makarantar da zai koyi karatun litattafai. Akasarin wannan karatun an fi yin sa ne a masallaci ko a gidan malamin da zai koyar.

Ilimin Gargajiya

[gyara sashe | gyara masomin]

Ilimin gargajiya ilimi ne wanda ake koyon shi akasari a wajen da ake aiwatar da shi. Misali idan anaso yaro ya koyi yarda ake wata sana'a kamar kira , noma , kafinta kokuma jima to ana zaunar da shi ne a inda ake aiwatar da ita wannan sana'a din. A haka har ya koya kuma ya iya. To amma dayake yanzu zamani ya can kuma al'amurra da yawa sun sauya, duk sauran abubuwan da ake koyo a gargajiyance a yanzu an zamanantar dasu. Misali ana koyon noma, kafinta, saka a makaranta tun daga matakin firamare har yazuwa Jami'a.

  • domin karin bayani jeka