Shinzō Abe (安倍晋三 Abe Shinzō, IPA: [abe ɕin(d)zoː]; An haife shi a 21 ga watan Satumba shekara ta 1954, shahararren dan siyasa kuma firayim minista na 63rd na kasar Japan kuma shugaban jam'iyar Leader of the Liberal Democratic Party (LDP) tun daga 2012, kafin nan shine na 57th da ke rike da ita tun daga shekara ta 2006 zuwa shekarar 2007. shine firayim minista na uku da suka fi kowa dadewa akan karagar mulki tun bayan yakin Japan.[1]
Mai Daraja
Shinzō Abe
安倍晋三, Shine Firayim minista na 57th a Kasar Japan mai ci a yanzu. Ya kama aiki daga 26 ga watan December shekara ta 2012 har zuwa 16 Satumba 2020.[1]
An haife da rada masa suna
安倍晋三 (Abe Shinzō) a 21 ga watan September shekara ta 1954 (shekarunsa 64)
Tokyo, Japan
Jam'iyar sa, Liberal Democratic
Matansa:
Akie Matsuzaki (m. 1987)
Wurin zamansa:
Kantei
Makarantar sa:
Jami'ar Seikei.
Abe yataso ne daga gidan yan'siyasa kuma an zabe shine a matsayin firayim minista na farko tun a watan satumban shekara ta 2006. A lokacin yana da shekara 52, yazama firayim minista mai karancin shekaru a kasar Japan tun bayan yakin Kasar kuma firayim minista na farko da aka Haifa bayan yakin duniya II. Abe yayi marabus a dalili na rashin lafiya a 12 ga watan September 2007, bayan kuma jam'iyarsa tayi rashin nasara a zaben kansiloli a wannan shekara. Yasuo Fukuda ne yagaje shi, Wanda na daya daga cikin firayim minista biyar da suka kasa dawowa ofishinsu fiye da watanni 16.
Abe ya dawo siyasa a 26 ga watan September shekara ta 2012, ya doke abokin takarar sa tsohon Ministan Tsaron Kasar, Shigeru Dan fafatwa a shugaban cin Kasar na jam'iyar LDP. Bayan samun nasara a jam'iyar ne a zaben 2012, yazama firayim minista na farko daya sake dawowa karagar mulki tun bayan Shigeru Yoshida a shekara ta 1948. An sake zabarsa a shekarar 2014 kuma da sake samun 2 cikin 3 na masu yawan al'ummah tare da abokin gamayyarsa Komeito, kuma yakara samun haka a zaben 2017.[1]